Labaran Hausa

Shari’ar Kano: Tsohon Ministan Shari’a Ya Zama Babban Lauyan Gawuna A Shari’ar Gwamnan Kano- Litepawa-News

Da Dumi Dumi Shari’ar Kano: Wanda Ya Buga da Yar’adua, Ya Kare El-Rufai a Kotu Ya Zama Lauyan Gawuna.

Akinlolu Olujinmi (SAN) ya tsayawa Nasiru Yusuf Gawuna a kotun daukaka kara a shari’ar zaben Gwamnan Kano.

Lauyan mai shekara 75 ya yi digiri a jami’ar jami’ar Obafemi Awolowo, su ne su ka kafa Olujinmi and Akeredolu a 1986.

A lokacin da Olusegun Obasanjo ya zama shugaban kasa, ya nada Olujinmi domin ya zama Ministan shari’a kuma AGF .

Abuja – Wanda yake tsayawa kare Nasiru Yusuf Gawuna a kotu a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano shi ne Cif Akinlolu Olujinmi (SAN).

A rahoton nan, Legit ta tattara ‘yan takaitattun bayanai game da Akinlolu Olujinmi (SAN), za a iya samu wasu bayanan a shafinsa na ICC.

An haifi Akinlolu Olujinmi ne a shekarar 1948 a garin Ibadan da ke jihar Oyo. Olujinmi ya yi karatun shari’a a jami’ar Obafemi Awolowo a Ile-Ife.

A shekarar 1979 aka kira Olujinmi zuwa makarantar koyon aikin lauyoyi. Bayan nan ai ya fara aiki a kamfanin NISER, daga baya ya koma UNIBADAN.

Zuwa 1986, Lauyan sun bude kamfaninsu mai suna Olujinmi and Akeredolu. Ofishinsu ya na titin Muhammadu Buhari a unguwar Garki a Abuja.

Olujinmi ya na cikin Lauyoyin da aka yi wa karin matsayi zuwa SAN a shekarar 1997. Samun lambar SAN na nufin ya gawurta a harkar shari’a.

Akinlolu Olujinmi, SAN ya rike Ministan shari’a na shekaru biyu tsakanin 2003 da 2005 a lokacin da Shugaba Olusegun Obasanjo ya ke mulki.

Lauyan ya maye gurbin Kanu Agabi SAN, bayan an cire shi kuma sai aka nada Bayo Ojo SAN.

Kwarewar Lauyan ta sa har ya taba gabatar da takarda a matsayin bako mai jawabi a zauren babban kotun Duniya watau ICC tun a 2005.

Akinlolu Olujinmi ne ya kai kara a lokacin da Ummaru ‘Yaradua ya bar Najeriya ya na shugaban kasa ba tare da ya nada shugaban rikon kwarya ba.

Lauyan ya tsayawa Cecelia Ibru lokacin da Sanusi Lamido Sanusi ya maka ta a kotu bayan ya zama Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN a 2009.

Da aka taso Nasir El-Rufai a gaba a Yulin 2009, lauyan ne wanda ya kare shi. An zargi tsohon Ministan da badakalar filaye da ya ke rike da Abuja.

Kafin yanzu, lauyan ya yi shari’a a kotu a matsayin lauyan zabe na APC, shi ne kan gaba wajen kare Biodun Olujunmi da aka yi zaben Gwamnan Ekiti.

Labari ya zo cewa Lauyan Abba Kabir Yusuf ya ce tun farko yin hukuncin zabe ta Zoom da aka yi domin raba gardama a Kano ya sabawa doka.

Wole Olanipekun ya na ikirarin ba ayi wa NNPP adalci a Kano ba, ya nemi a soke nasarar APC, inda Olujunmi ya zargi jam’iyya mai-ci da magudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button