Labaran Hausa

Da Dumi Dumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tanadi hukunci kan rikicin zaɓen gwamnan Kano.

Da Dumi Dumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta tanadi hukunci kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar, ya na kalubalantar tsige shi da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi.

Kotun, wacce ta yanke hukuncin ta hanyar manhajar Zoom, ta soke nasarar Yusuf, inda ta ayyana dan takarar APC, Nasiru Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hakan ya sanya gwamnan ya garzaya kotun daukaka kara domin kwato hakkinsa.

Amma bayan sauraron karar a yau Litinin, kotun ta ajiye hukunci kan karar.

Bayan sauraron muhawarorin manyan lauyoyin jam’iyyun, alkalan sun gargadi bangarorin da kada su tuntube su a kan hukuncin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button