Labaran Hausa

Salon da Hisba ke bi ya saɓawa Musulunci “bai kamata Malam Daurawa ya zura ido ana cin zarafin mutane da sunan gyara ba”

“Dalibai na cikin haɗari a Kano” -Salon da Hisba ke bi ya saɓawa Musulunci “bai kamata Malam Daurawa ya zura ido ana cin zarafin mutane da sunan gyara ba”

Daga Wakiliya

“Bai kamata malamin da ya yi shuhura wajen ba da fatawa da tarbiyya irin Sheikh Aminu Daurawa ya bari, ko ya ba da umarnin cin zarafi da keta mutunci da tozarta ɗan’adam da sunan kawo gyara ba”

Daliban dake karatu a jihar Kano suna cikin fargaba saboda yadda ake zargin jami’an Hisbah suna kutsawa har gidajen kwanan Dalibai suna kamo su da sunan sun kama ƴan baɗala, “wallahi tallahi har cikin gida suka balla kofa suka shigo suka kama ƴan’uwanmu dalibai, suka tafi dasu”

“Tun daren jiya muke bin diddigi amma sun ƙeƙashe ƙasa sun ƙi sakinsu, yau sun kaisu ofishin yan sanda amma da alama DPO yaƙi rubuta masu takardar shigar da ƙara da suka je nema, domin DPO ya ce bai san laifin da zai rubuta mutanen sunyi ba, kuma ba shi ya kamo su ba”

Wakiliya ta ruwaito daga bisani yan Hisban sunyi amfani da motoci sun kwashi mutanen sun kaisu hedikwatarsu za su gurfanar dasu a gaban kotun su

Masu sharhi na ganin wannan holin da Hisba ke yi wa mutanen da ta kama, ya keta dokar Musulunci, sannan ita kanta dokar da ta kafa Hisba ma, ba ta ce a yi haka ba.

Wani mai sharhi Ali Jamilu ya ce “samamen da Hisba ta yi, da kame da bulala har da holin mutanen ga ƴan jarida, tozarta ɗan’adam ne wanda hakan ya saɓa wa Musulunci da karantarwar Annabi (SAWS).

Kuma babu inda dokar da ta ƙirƙiri hukumar ta ba su damar yin hakan”.

“Bai kamata malamin da ya yi shuhura wajen ba da fatawa da tarbiyya irin Sheikh Aminu Daurawa ya bari, ko ya ba da umarnin cin zarafi da keta mutunci da tozarta ɗan’adam da sunan kawo gyara ba”.

Ya ce “kamata ya yi kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin jihar Kano ya ja hankalin hukumar Hisbar, don su san matsayinsu a dokar da ta ƙirƙiri hukumar”.

“Muna ba da shawara a riƙa aiki da lura da bin doka da oda, ba wuce gona da iri ba, wanda hakan ya saɓa dokokin musuluncin da ake iƙirarin ana yi don shi, haka nan ya saɓawa dokokin ƙasa da kundin tsarin mulkin Najeriya”, in ji Ali Jamilu

Wakiliya ta tuntuɓi hedikwatar hukumar Hisbah a jihar Kano domin jin ta bakinsu akan waɗannan zarge-zarge da ake masu amma sun ce “za su binciki lamarin su neme mu domin bamu amsa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button