Labaran Hausa

Waze Biya,? Ana Tsaka da Jimamin Korarsa a Gwamnan Kano, Abba Ya Tura ’Ya’yan Talakawa 150 Karatu a India.

Akalla Kanawa 150 ne suka samu cikakken tallafin karatu don ci gaba da karatun digiri na biyu a waje.

Tallafin da aka ba wadannan dalibai ya samu amincewar Gwamna Abba Yusuf bayan da kotun daukaka kara ta soke zabensa.

An tattaro cewa an zabo wadannan dalibai ne daga cikin dalibai 1,001 ‘yan asalin jihar Kano da ke fadin kananan hukumomin jihar Kano.

Jihar Kano – Biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na soke zabensa, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aike da rukuni na hudu da ya kunshi dalibai 150 zuwa kasar India don yin digiri na biyu.

Daliban sun tafi India ne daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano kafin a bayyana hukuncin kotun, wanda ya tabbatar da hukuncin da kotun kararrakin zabe da ta ba Gawuna gaskiya.

Sai dai duk da wannan koma-baya, Gwamna Yusuf na NNPP ya bukaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwar zai yi nasara a kotun koli, rahoton PM News.

A cewar gwamnati, an zabo daliban 150 ‘yan asalin jihar Kano 1,001 domin daukar nauyinsu su yi digiri na biyu a kasashen waje, rahoton Tribune Online ta ruwaito.

Wannan na daga cikin shirin ba da tallafin karatu da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kawo a farkon fara mulki.

Ba wannan ne karon farko ba, gwamnatin Kwankwaso, uban gidan Abba Kabir Yusuf ya sha ba da guraben karatu kyauta ga matasa a fadin jihar mai yawan jama’a.

A wani labarin, Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce ya sanar da lauyoyinsa da su garzaya zuwa kotun koli kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke.

A ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamba ne kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta yanke.

Kotun ta tsige Yusuf dan takarar jam’iyyar NNPP a matsayin gwamnan jihar Kano, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button