yanzu-Yanzu: Kamar dai yadda kuka sani ƴan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.
Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.

Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga ƴan mata da samari na yin abubuwan da zasu ɗauki hankulan abokansu na sada zumunta.
Wata budurwa mai suna Zainab Abdull ta bayyana cewa “Gaskiya ina son mutum na gari ya aureni ban damu idan kai talakane ba” kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter ga hoton Screenshot ɗin rubutunta nan daga ƙasa.
