Labaran Hausa

Yadda Ake Sauraron Shari’ar Zaben Abba Gida Gida v Nasiru Gawuna a Kotu (Kai-Tsaye)

Abuja – A safiyar Juma’a, kotun daukaka kara mai zama a birnin tarayya watau Abuja za ta yanke hukunci a shari’ar zaben Gwamnan jihar Kano.

Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602 a zaben da aka yi, Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya zo na biyu ya samu kuri’a 890,705.

Da APC ta je kotun daukaka kara, Alkalai sun rage fiye da 165, 000 daga cikin kuri’un NNPP saboda rashin sa hannu da hatimi, aka ba APC nasara.

Shari’ar nan ne Abba Kabir Yusuf ya kalubalanta a wannan kotu, APC kuma ta roki a tabbatar da hukuncin da karamar kotun zaben ta zartar a Satumba.

Bayan sauraron shari’ar, Alkalan kotun daukaka kara sun tsige Abba Kabir Yusuf bisa dalilali da hujjojin jam’iyyar APC.

Kotun daukaka kara ta sake ba Kotun korafin zabe gaskiya da ta ce Abba Kabir Yusuf ba cikakken ‘dan jam’iyyar NNPP ba ne.

Premium Times ta rahoto cewa kotun daukaka kara ta ce ya kamata a rusa takarar Abba a jam’iyyar NNPP tun a karamar kotu.

Kotun ta zartar da cewa yin hukunci ta Zoom a maimakon a zauna a harabar kotu ba laifi ba ne, an yi watsi da korafin Wole Olanipekun.

Barista Hikima wanda yake kawo bayanai daga kotun ya rubuta a shafinsa cewa kotu ta ce:

“Ba dole bane sai APC ta saka sunan Nasir Gawuna wajen shigar da kara ba.” –

Kotun daukaka kara ta ce karamar kotu ba ta saba doka da ta karbi takardun da lauyoyin jam’iyyar NNPP su ke adawa da su ba.

Majiya daga kotun daukaka karan ta ce Alkalai sun fara karanto hukunci, an soma yin shimfidar korafin lauyoyin Gwamnan Kano.

Kamar yadda Barista Hikima ya fada a shafinsa, hukunci hudu za a yanke a zaman yau; uku daga NNPP sai kuma guda daga APC.

Abba Hikima wanda shahararren matashin lauya ne a Kano, ya fada a Facebook cewa an baza jami’an tsaro kafin a fara shari’ar.

A Kano ma an dauki matakai masu tsauri domin gudun rikicin siyasa ya barke.

Ibrahim Arif Garba wani lauya ne wanda yana kotun domin jin shari’ar zaben Gwamnan na Kano,

ya shaida cewa an fara zama. Kamar yadda sanarwa ta zo, zuwa karfe 10:00 ko kimanin haka za a fara hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button