Labaran Hausa

Abba vs Gawuna: Kotun Daukaka Kara Ta Sanya Ranar Fara Sauraron Shari’ar Gwamnan Kano.

Kotun ɗaukaka ƙara ta sanya ranar fara sauraron ɗaukaka ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kan zaɓen gwamnan Kano.

Kotun ta sanya a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za ta fara sauraron ƙarar da Gwamna Abba ya ɗaukaka

Gwamna Abba ya ɗaukaka ƙara ne bayan kotun zaɓe ta tsige shi daga muƙamin gwamnan Kano tare da bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

Kotun daukaka ƙara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba domin sauraron ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya ɗaukaka.

Gwamna Abba Kabir ya ɗaukaka ƙara kan abokin takararsa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nasiru Yusuf Gawuna, bayan kotun zaɓe ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kano, cewar rahoton jaridar Daily trust.

Gwamnan ya shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar soke zaɓensa da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta yi, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ta tsige Yusuf a ranar 20 ga Satumban 2023, ta hanyar bayyana ƙuri’unsa 165,663 a matsayin marasa inganci saboda “ba INEC ta sanya hannu ko ta buga musu tambari ba.”

Ɓangarorin da ke cikin ƙarar sun haɗa da Gwamna Yusuf da jam’iyyarsa, NNPP da jam’iyyar adawa ta APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

INEC ta bayyana Gwamna Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na ranar 18 ga watan Maris, 2023 bayan ya samu ƙuri’u 1,019,602 yayin da Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.

Sai dai, da kotun ta cire ƙuri’u 165,663 daga ƙuri’un Gwamna Yusuf inda ƙuri’unsa suka koma 853,939, ƙasa da 30,000 na ƙuri’u 890,705 da Gawuna ya samu.

Sakamakon haka, kotun ta bayyana ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna tare da umartar hukumar zabe ta INEC da ta janye takardar shaidar cin zaɓen Gwamna Yusuf.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button