Labaran Hausa

Da Dumi Dumi: Dakarun Sojin Najeriya Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 100, Sun Samu Nasarori Masu Yawa.

Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta’adda 113, kuma sun kamo wasu 300 a makon da ya gabata a faɗin kasar nan.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce bayan haka sojojin sun kwato mutane 91 da aka yi garkuwa da su.

A cewarsa, wannan karon an samu haɗin kai tsakanin sojojin sama da na ƙasa irin wanda ba a taɓa samunsa ba.

FCT Abuja – Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta samu nasarar murƙushe ƴan ta’adda 113 tare da kamo wasu 300 a cikin mako ɗaya a sassan ƙasar nan.

Bayan haka, Dakarun sojin sun kuma ƙwato mutane 91 da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a wannan lokaci, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana waɗannan nasarori a wata sanarwa da ya fitar jiya Alhamis a Abuja.

Buba ya kuma bayyana cewa sojoji sun kama mutane 25 da ake zargin ɓarayin ɗanyen man fetur ne, tare da lalala haramtattun matatun mai 49 a makon jiya.

Kakakin sojin ya yi bayanin cewa bayan haka sun kuma yi nasarar ƙwato man da ɓarayin suka sace wanda ya kai kimanin N571,793,350.00.

Ya ce sojojin sun ƙara da kwato makamai iri-iri guda 129 da alburusai kala daban-daban guda 717 daga hannun ƴan tada ƙayar baya, rahoton PM News ya tattaro.

Janar Buba ya ce dakarun sojin kasar za su ci gaba da matsa wa kungiyoyin tada ƙayar baya lamba da nufin samar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Najeriya.

Kakakin sojin ya ce: “Ko shakka babu dole ne a ci galaba a kan wadannan kungiyoyi, kuma lalle ana cin nasara a kan su.”

“Saboda wadannan dalilai ne muke yiwa ‘yan ta’adda, ‘yan tada kayar baya da masu tsattsauran ra’ayi mummunar barna ta hanyar samamen da muke kai musu a fadin kasar nan.”

“An samu haɗin kai tsakanin sojojin sama da na ƙasa kamar wanda ba a taɓa gani ba kuma yana haifar da sakamako da nasarori masu ban mamaki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button