Labaran Hausa

Da Dumi-Dumi Daurawa Ya Tona Asiri Bisa Kame Da Hizba a Kano Takeyi…Litepawa-News

TSAFTACE KANO DAGA BAƊALA: Ba Ma Kwanmu Sai Da Zakara, Ma’ana Sai Mun Yi Bincike Muke Kai Sumame, Cewar Sheikh Daurawa

Daga Imam Aliyu Indabawa.

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah a jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi martani ga masu caccakar ayyukan hukumar yana mai cewa hukumar tana aiki ne bisa doron doka da oda.

Ya bayyana cewa hukumar Hisbah ba ta kai sumame haka kawai ba tare da bincike na ƙarƙashin ƙasa ba bayan hukumar ta karɓi ƙorafi daga mazauna kusa da wurin, kuma bayan tabbatar da ƙorafin tana bin duk wata ƙa’ida cikin ayyukan nata.

A yayin tattaunawarsa da kamfanin watsa labarai na BBC Hausa ya ce mafi yawan matan sun kwararo ne zuwa Kano daga jihar Gombe da Borno wanda ba da jimawa ba gwamnonin jihohin suka fatattaki karuwai daga jahohin nasu.

Ya kuma bayyana cewa talauci ya yi tasiri wajen yawaitar karuwanci da baɗala, don haka ne hukumar ke ta samun koke-koke da ƙorafin yadda a ke shige da fice da ƴan mata daga mutanen da ke kusa da inda abubuwan ke faruwa.

Ya ce, ” kafin mu fita sumame sai mun sanar da DPO lokacin zuwan namu. Sannan idan ba ka yi operation lokacin da a ke laifi ba, ba za ka kama mutum yana laifi ba, saboda haka shi ya sa mu ke fita tsakiyar dare wanda babu wata macen arziki da za a ganta tana yawo a titi a wannan lokacin. Daga goman dare mu ke fara bibiyar waɗannan wuraren, kuma ba ma fita sai mun karɓi warrant ‘izni’ na shiga wuraren da a ke laifin. Akwai abubuwan ma da ba mu nuna ba saboda kare mutuncin masu laifin.

“Sannan ba iya mata kaɗai muka kama ba har da maza akwai ƴan Kano akwai kuma yan wajen Kano. Akwai waɗanda aka same su a cikin wurin, akwai waɗanda aka same su sun fito, wasu kuma an same su suna ƙoƙarin shiga,

“Game da waɗanda aka kama, na farko za mu yi musu wa’azi mu faɗakar da su mu yi musu gargaɗi kamar yadda mu ke yi wa masu otel ɗin ma muna gayyatarsu mu faɗa musu cewa bai kamata a yi hotel don cin abinci ko kwana, amma kuna gani ana zuwa da mata ana lalata da su a otel ɗinku ba.

“Mataki na biyu idan muka ga wacce aka taɓa kamo ta sau biyu ko sau uku ko sau biyar sai mu miƙa ta kotu wurin Alƙali domin ya yi mata hukuncin laifin da ya bayyana a gareshi na laifin da mu ke zargin ta aikata.”

Tun da hukumar ta fara sumamen kawar da baɗala al’umma ke ta cece-ku-ce, a yayin da wasu ke yabon ayyukan, wasu kuma suna ganin akwai cin zarafi a cikin ayyukan hukumar, to sai dai masu wannan ra’ayi sun kasa tabbatar da iƙirarin nasu da hujja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button