Labaran Hausa

DA DUMI-DUMI: Hisbah ta gayyaci Murja Kunya da takwarorinta yan Tiktok su kai kansu.

A wata sanarwa da hukumar Hisba ta jihar Kano ta fitar ta ce gayyatar ya haɗa da kowa da kowa,

“Fitaccen malamin addinin musulunci a Nijeriya kuma shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano, Sheikh Imam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa na gayyatar ƴan Tiktok zuwa hukumar Hisbah da ke kan titin Sharaɗa Kano”

Wakiliya ta ruwaito Hukumar ta gayyaci ƴan Tiktok din ne domin yin zama na musamman da Sheikh Daurawa a ranar litinin mai zuwa 6-11-2023 da misalin ƙarfe huɗu na yamma”

Gayyatar dai na zuwa ne bayan masu amfani da kafafen sadarwa na ta kiraye-kiraye ga hukumar ta tsawatawa yan Tiktok musamman taurarin Tiktok irinsu Murja Ibrahim Kunya, Mai Wushirya, Al-Ameen G-Fresh da sauransu waɗanda ake ganin ya kamata hukumar ta kwabesu akan yadda suke gudanar da ayyukansu akan shafin Tiktok.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button