Labaran Hausa

Da Dumi Dumi Hujjojin Abba Kabir Yusuf Da Kotu Zata Duba Wajen Ruguza Nasarar Gawuna.

Abba v Gawuna: Abubuwa 13 da Kotun Daukaka Kara Za Ta Duba a Shari’ar Zaben Gwamnan Kano .

Kotun daukaka kara ta fara sauraron shari’ar da Abba Kabir Yusuf ya gabatar a kan zaben Gwamnan jihar Kano na 2023

Gwamnan ya na mai kalubalantar hukuncin da kotun sauraron korafin zabe wanda ya tsige shi daga kan kujerar da yake kai.

Lauyan da ya tsayawa Abba Yusuf, Wole Olanipekun ya gabatar da jerin korafi sama da 40 da yake so babban kotun ta duba.

Jaridar Legit ta jero muhimmai daga cikin korafin da Wole Olanipekun SAN ya mikawa kotu a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf a Abuja.

An gabatar da hujjoji a ranar 22 ga watan Yuli 2023 bayan an rufe kofar yin hakan a ranar 15 ga watan Yuli 2023 har an fara kira shaidar wanda ake kara.

Wole Olanipekun ya yi ikirarin cewa ya kamata kotu ta zauna ne kamar yadda ta rika sauraron korafin a baya, amma a karshe sai aka yi shari’a ta kafar Zoom.

Lauyoyin APC ba su fadawa kotu yadda Nasiru Yusufu Gawuna ya samu 25% a biyu bisa ukun kananan hukumomin Kano, wanda wajibi ne a sashe na 179(2).

A cewar lauyan da ya tsayawa Gwamna, babu takardar karatu da aka gabatar mai nuna wanda ya bada shaida masani ne, akasin abin da dokar shaida ta bukata.

Masu korafi sun ce lauyoyin APC sun kawo marasa jin Turanci domin bada shaida duk da Ingilishi ne yaren kotu, su ka bukaci a rusa shaidar wadannan mutane.

Karar Wole Olanipekun ta kara da cewa kotun korafin zabe ba ta bi ka’idar da aka yanke a game da ratar lashe zabe ba, inda aka ce APC ta bada tazarar kuri’u 36, 719 .

Fitaccen lauyan ya yi ikirarin Alkalan da su ka fara sauraron shari’ar zaben Kano ba su yi amfani da dokar kasa da dokar bada shaida wajen karbar shaidun APC ba.

NNPP ta zargi Kotu da cewa ita ta ba kan ta aikin sokewa Abba Kabir Yusuf kuri’u duk da babu dalilin yin haka a doka, kuma ba a bukaci NEC ta kare kan ta ba.

Idan aka duba sashe na 63 na dokar zabe, Olanipekun ya ce babu inda aka wajabta rubutu sunan malamin zabe, hatimi da kwanan wata, don haka an cire kuri’un halal.

A madadin Gwamna Abba, lauyoyi sun ce ba a kira wakilan jam’iyya su bada shaida daga rumfuna ba, kuma doka ba ta bada damar bambanta kuri’un NNPP da APC ba.

Ana da labari Lauyoyi irinsu Femi Falana SAN da Barista Kabir Akingbolu sun soki hukuncin Alkalai a shari’ar Gwamnan Kano, su ka ce ba ayi adalci ba.

Kabir Akingbolu Esq ya shaida cewa hukuncin shari’ar zaben Shugaban kasa (PDP da LP vs APC) ya nuna kuskuren da aka tafka a zaben jihar Kano na 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button