Labaran Hausa

Kano: Yan Bindigan Boko Haram Sun Kai Hari Jahar Kano Sojoji Sun Musu…

Kano: Ana cikin tsoro a jihar Kano bayan jami’an tsaro sun dakile wani harin Boko Haram a jihar Kano.

Rundunar sojin Najeriya da hukumar DSS sun yi nasarar dakile harin ne a karamar hukumar Gezawa da ke jihar.

Daraktan yada labarai na rundunar, Onyema Nwachukwu shi ya tabbatar da haka a yau Juma’a 3 ga watan Nuwamba.

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Rundunar sojin Najeriya da hukumar DSS sun yi nasar dakile harin Boko Haram a jihar Kano.

Wannan na cikin wata sanarwa ce da daraktan yada labarai na rundunar, Onyema Nwachukwu ya fitar a yau Juma’a 3 ga watan Nuwamba.

Rundunar ta ce an kai samamen ne a safiyar yau Juma’a 3 ga watan Nuwamba inda ta kwace muggan makamai a hunnun ‘yan ta’addan.

Onyema ya ce rundunar ta yi nasarar dakile harin ne a karamar hukumar Gezawa da ke cikin jihar,

cewar Punch. Ya ce yayin samamen, sun yi nasarar cafke wasu da ke zargi mutum biyu tare da kwato muggan makamai a hannunsu, cewar The Nation.

Sanarwar ta ce:

“Jami’an hadin gwiwa ta sojoji da hukumar DSS sun yi nasarar dakile harin Boko Haram a Kano.

“A wata samame da rundunarmu ta kai da jami’an DSS, mun yi nasarar dakile harin a karamar hukumar Gezawa da ke jihar.

“Har ila yau, rundunar ta yi cafke wasu mutum biyu da ake zargi inda aka kwato muggan makamai a hannunsu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button