Labaran Hausa

Tofa-Zaben Kano: Shugaba Tinubu Ya Shiga Babbar Matsala Kan Tsige Gwamna Abba Gida-Gida

Da Dumi Dumi: Ƙungiyoyi da wasu jagororin siyasa sun gargaɗi shugaban kasa, Bola Tinubu, ya guji neman tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano

Wata kungiya mai rajin kawo ci gaba ta yi gargaɗin cewa sauke Gwamnan daga mulki ka iya tarwatsa siyasa da haɗin kan Najeriya.

Kotun zaɓe ta tsige Gwamna Yusuf kana ta ayyana Nasir Gawuna a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Kano, yau Kotun ɗaukaka ƙata zata yi hukunci

FCT Abuja – Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na fuskantar matsin lamba kan ya amince da sakamakon zaɓen Gwamnan jihar Kano wanda aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Shugaba Tinubu na shan matsin lamba kan kujerar Gwamnan Kano ne domin daidaito da adalcin siyasa da kuma samun haɗin kai mai ɗorewa a Najeriya.

A rahoton jaridar Leadership, wasu jagororin siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu ne suka buƙaci haka ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2023.

Wannan na zuwa ne yayin da Kotun ɗaukaka ƙara ke shirin yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar da ta kalubalanci hukuncin Kotun zaɓe wadda ta tsige Abba Kabir Yusuf.

A wurin taron tattaunawa na ƙungiyar rajin kawo ci gaba (FNID) ƙarƙashin Oguntade Omolewa, ƙungiyar ta gargaɗi Tinubu ya daina bin haramtaciyar hanya da nufin tsige Abba Gida-Gida.

Yusuf, ɗan takarar jam’iyyar NNPP ya samu nasara kan babban abokin karawarsa na APC, Nasir Gawuna a zaben da ya gabata kuma INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓe.

A halin yanzu, Kotun ɗaukaka kara ta shirya yanke hukunci wanda zai zama raba gardama a karar da Gwamna Yusuf ya ɗaukaka yana kalulabalantar tsige shi da aka yi.

A wani rahoton na daban Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Abdulrasheed Shehu, ya yi hasashen wanda zai samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara kan zaben Kano.

Jigon jam’iyyar PDP ya bayyana cewa lissafin da ke gaban APC shi ne ta maida Najeriya hannun jam’iyya ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button