Labaran Hausa

Bidiyo: Hukunchin Masu Shan Maganin Karfin Maza Don Su Wahalar Da Matan su.

Ash Sheikh Dr. Abdallah usman Gadon kaya yayi nasiha da jan hankali ga ma’aurata akan shan maganin gargajiya ko dai wane iri ne na karfin maza domin jin kuzari wajen gamsar da uwar gida a yayi kwanciyar aure.

Danna Nan 👇👇👇👇


Wannan abun yanzu ya zamo ruwan dare domin mutane wasu sunfi son su ja har sai ta waye haba dai malam kamar jaka.

To shine cikin wanann karatu ash Sheikh Dr.abdallah usman Gadon kaya yayi nasiha da jan kunne inda aika hakan da wasu ke yi ya wuce gona da iri kamar yadda malamin ya bayyana a cikin wani faifan bidiyo, da anka wallafa a shafin @khamis_ali_musa_abdullah a shafin tiktok.

“Duk namiji da zai maganin gargajiya domin ya azabtar da matarsa wallahi haram ne mutum ya tsaya akan sarikarsa karfin da Allah ya bashi, magani da zai ƙara maka nishadi ba laifi maganin da zai ƙara maka lafiya ba laifi, amma mutum yaje ya sha maganin da zai fitar da shi daga daidai hallitar da Allah yayi masa , ya koma kamar doki ko zaki kawai ya gajiyar da mace.

Yasa ta ihu yasa ta wahala wannan bai dace ba miye dalilina duk abinda yake cutarwa bai hallata kayiwa dan uwan ka ba, yanzu idan kaine yadda ake figa zakarin da zafi a lokacin zaka yadda kayi bazaka yi ba, taya zaku zo kuna saduwa da mata kamar dabbobi.

Mutum ya zamo doki kamar yana saduwa da goɗiya, kamar taure yana bin ƴar akuya wannan ba dai-dai bane,shaye shayen magani da ake ya kamata aji tsoron Allah”- inji Dr.Gadon kaya.


Malam yayi nasiha tare da kira ga hukuma ta sanya ido akan masu wannan sana’a zaku iya saurarin cikakken bayani ga bidiyon nan.

Malam yayi nasiha tare da kira ga hukuma ta sanya ido akan masu wannan sana’a zaku iya saurarin cikakken bayani ga bidiyon nan.

https://vm.tiktok.com/ZM6D6NDU1/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button