Labaran Hausa

Da Dumi Dumi: Mummunan Hukunchin Da Yan Bindiga Suka Fara Yiwa Yan Arewachin Nigeria Ya Munana Kamar Haka.

da Dumi Dumi: Ƴan bindiga na tursasa wa manoma biyan haraji kafin girbi a arewacin Najeriya.

Danna Nan 👇👇👇👇👇

Manoma a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce suna cikin halin tsaka mai wuya Sakamakon yadda ‘yan bindiga suke hana garuruwa da dama na yankin yin girbi da kwashe kayan amfanin gona.

Manoman sun ce ‘yan bindigar kan tilasta masu biyan zakkar amfanin gona da biyan kudi ko kuma idan ba haka ba su kwashe kayan amfanin gonar, ko su kone su kurmus.

Wani rahoto da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce za a fuskanci a yunwa a arewacin Najeriya sakamakon matsaloli da suka kunshi har da tsaro a yankin.

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta yi zama da shugabannin mutanen yankin kan yadda za a shawo kan matsalar tsaron.

Mazauna yankin Birnin Gwari sun ce matsalar ta yi kamari musamman yadda ɓarayi suka addabe su.

“Ƴan bindigar za su zo ana cikin aikin gona su koma gefen su kasa su tsare bayan an gama tattara amfanin gona an saka a buhu su ce nasu ne.”

“Sannan za su ce a saya a ba su kuɗin bayan tattara amfanin gonar,” kamar yadda wani mazauni yankin Birnin Gwari ya shaida wa BBC.

Ya ce manomi ba zai iya kwashe amfanin gonarsa ba har sai ya kammala biyan harajin da ɓarayin suka aza masa.

“Idan kuma mutum ya gaza biyan kuɗin da suka buƙata, sai dai ya bar amfanin gonar a nan.”

“Akwai kuma ƴan Ansaru waɗanda ke tilata wa manoma biyan zakka, baya ga ƴan bindiga da ke kwashe amfanin gona”

“Wannan matsala ta tilasta wa mutane da dama yin gudun hijira.” in ji shi.

A jihar Katsina ma akwai ƙauyuka kusan shida da ƴan bindigar suka tilasta wa biyan kuɗin tara, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.

“Sun aza wa ko wane gari naira dubu ɗari bakwai da ashirin,” a cewar wani mazauni yankin wanda ya ce ɓarayin sun tilasta masu biyan kuɗi kafin girbe amfanin gonarsu

Ya ce kowane gari idan ya haɗa za a tafi a kai wa ɓarayin .

Matsalar hana girbi da kwasar amfanin gona da yan bindiga ke yi a yankin arewacin Najeriya wani ƙarin ƙalubale ne ga batun samar da abinci a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke kukan matsalar matsin tallalin arziki.

Rahoton hukumar samar da abinci ta majalisar ɗinkin duniya ya ce mutum sama da miliyan 16.5 ke fuskantar barazanar yunwa a yankin arewacin Najeriya daga Oktoba zuwa Disamban 2023.

Sannan matalar za ta fi ƙamari a 2024 inda mutum miliyan 26 za su fuskanci barazanar yunwa a yankin na Najeriya da ta fi arziki a Afirka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button