Labaran Hausa

Da Dumi Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari a Jihar Zamfara, Sun Yi Awon Gaba da Mutum 5.

Da Dumi Dumi: Miyagun yan bindigan a yayin harin da suka kai sun kuma kona wata motar sintiri ta yan sanda kurmus

Mazauna garin Maru sun koka kan yadda yan bindiga ke addabarsu da hare-hare ba kakkautawa a garin

Jihar Zamfara – Wasu yan bindiga dauke da makamai

sun kai hari a garin Maru hedikwatar karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Yan bindigan a yayin harin sun kashe mutum daya, sannan suka kona wata motar yan sanda da ke sintiri a kan titi, sannan suka yi awon gaba da mutum biyar ciki har da wani malami na Kwalejin Ilimi (COE) ta Maru.

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar wadanda suka zo da yawa sun afkawa garin Maru da safiyar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba da nufin yin awon gaba da mazauna garin.

Wani mazaunin garin Malam Yusuf Musa ya shaida wa jaridar Nigerian Tribune cewa yan bindigar sun isa garin Maru dauke da manyan makamai.

“Lokacin da suka shiga garin, sai suka fara harbi lokaci- lokaci domin tsoratar da mutane.” A cewarsa.

Bugu da kari, Mallam Mohammed Amadu, dan asalin garin, ya bayyana cewa:

“Yan bindigan wadanda suka zo da yawa, sun dira garin cikin dare inda suka farmaki al’umma. Da yawa daga cikinmu mun gudu zuwa cikin daji domin tsira daga harin.”

“An sace mata uku da maza biyu da suka hada da Lawali Dan Muazu da Nasiru Anka malami a Kwalejin Ilimi ta Maru.”

“Ƴan bindigan waɗanda suka zo da yawa, sun dira garin cikin dare inda suka farmaki al’umma. Da yawa daga cikinmu mun gudu zuwa cikin daji domin tsira daga harin.”

“An sace mata uku da maza biyu da suka haɗa da Lawali Dan Muazu da Nasiru Anka malami a Kwalejin Ilimi ta Maru.”

Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda yace mutanen garin Maru na fuskantar hare-hare ba kakkautawa daga ƴan bindiga. A cewarsa harin na yau shi ne karo na uku cikin kwanaki 11.

Ya koka da cewa ƴan bindigan sun kuma halaka wani mai gyaran waya mai suna Abdul, wanda ke da shago a babbar kofar shiga tashar motan Maru.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ba, saboda kiran da aka yi masa ta wayarsa da dama bai amsa ba, kuma an kashe layukan wayarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button