Labaran Hausa

Miji ya rasu bayan amaryarsa ta kwana da tsohon saurayinta kwana biyu da auren su…👇👇

Wani matashi a kasar Ghana mai suna Shadrack Boadu wanda aka fi sani da Owura ya rasu sakamakon wata gajeriyar rashin lafiya da yayi wacce ake kyautata zaton sakamakon bugun zuciyar da ya samu ne saboda takaicin abunda amaryarsa tayi masa.

Danna Hoton Nan 👇👇👇

Mahanga ta ruwaito gabanin rasuwarsa Owura ya ɓulla a wani shirin talbijin yana bayyana cewa, babban tashin hankalin da yake ciki a yanzu shine yadda ya gano matarsa Louisa ta yi lalata tare da tsohon saurayinta Alex kwanaki biyu kacal da aurensu.

A cewar Owura, tun bayan wannan cin amana da matarsa ta yi baya da wata natsuwa kuma auren nasu ya shiga tangal-tangal. Kodayake a wani bincike an gano cewa dama auren dole aka yi masu kuma Lousia bata sonshi,

Bayanan sun nuna duk lokacin da ya fuskance ta takan taka masa burki kuma ta sha nanata masa cewa tausyinsa kawai yasa ta aure shi amma bata son shi, a wasu lokutan ma takan yi kururuwar ya sake ta domin ta koma ga soyayyarta ta asali wato tsohon saurayinta da take so.

Wata kafar yada labarai a Ghana ta ruwaito yadda margayin ke ƙorafi cewa “Louisa ta sanya rayuwa a duniya ta zama kamar Jahannama a gare shi, babban abunda ke ci masa tuwo a ƙwarya shine yadda surukarsa take goyon bayan ‘yarta”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button