Labaran Hausa

Qalu Innnalillahi Rikicin Fulani Da Yan Bijilanti Yayi Sanadiyar Mutuwar…

Da Dumi Dumi: Mutane 2 sun rasu a rikicin da ya barke tsakanin ƴan bijilante da makiyaya a Neja.

An tabbatar da mutuwar mutane 2 sannan bakwai suna kwance a asibiti, sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin Fulani makiyaya da ƴan bijilante a kasuwar mako-mako da ke garin Beni a karamar hukumar Bosso ta jihar Neja.

Wani mazaunin yankin ya shaidawa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma a ranar Laraba, lokacin ana tsaka da hada-hada a kasuwar.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, mataimakin shugaban ma’aikatan lafiya na cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Beji, Aliyu Yusuf, ya ce an kawo mutane tara zuwa asibiti da raunuka daban-daban.

Sai dai ya ce an tabbatar da mutuwar biyu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, yayin da sauran bakwai da aka jikkata, dukkansu Fulani, suna karbar magani.

A halin da ake ciki, Kwamishinan kula da Makiyaya na Jihar Neja, Umar Rabe Sanda, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi gargadi kan duk wani nau’in harin ramuwar gayya.

A cewarsa, gwamnatin jihar za ta hada hannu da duk masu ruwa da tsaki wajen ganin an warware rikicin Fulani da manoman Gbagyi.

Ya kuma gargadi bangarorin biyu da su daina daukar doka a hannunsu, yana mai cewa akwai hanyoyi daban-daban na warware takaddama ba tare da tayar da hankali ba.

Mataimakin shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria Zone B, Abdullahi Mu’azu, ya ce rikicin ya kawo cikas ga harkokin kasuwar a ranar Larabar da ta gabata, inda ya yi kira ga hukumomi da su sa baki domin ganin lamarin bai sake faruwa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button