Labaran Hausa

Da Dumi Dumi Burutai Ya Tona Asiri Kan Ta’addanchi A Nigeria Ga Duk Abin da…

Tsaro: Tukur Buratai Ya Fasa Kwai Kan Ainihin Wadanda Suka Kawo Rashin Tsaro a Najeriya.

Laftanar Janar Tukur Buratai ya yi magana kan rashin tsaron da ya dade yana addabar ƙasar nan.

Tsohon babban hafsan sojin ƙasan ya bayyana cewa ƴan siyasa ne suka samar da rashin tsaro a ƙasar nan.

Buratai ya kuma caccaki waɗanda suka riƙa sukarsa kan matsalar tsaro lokacin da yake a bakin aiki.

Tsohon babban hafsan sojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Tukur Buratai, ya ce rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi, ƴan siyasa ne suka samar da shi.

Buratai ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 3 ga watan Nuwamba, yayin wata lakca da aka shirya domin bikin cika shekaru 65 da kafa kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Ibadan, cewar rahoton Daily Trust.

Ya kuma yi kakkausar suka ga masu sukar sa da ke kira da a kore shi saboda rashin tsaro a ƙasar a lokacin da yake kan mulki, yana mai cewa irin wannan kiran ya samo asali ne daga son zuciya maimakon tantance haƙiƙanin aikinsa, rahoton Guarɗian ya tabbatar.

A kalamansa:

“Waɗannan mutanen ta yiwu suna da wani ra’ayi mara kyau kan Buratai bisa wasu dalilai da suka haɗa da son zuciya ko son rai waɗanda ba su da alaƙa da abin da zai iya yi.”

“Yana da kyau a fuskanci rin waɗannan batutuwan kan tsaron ƙasa da zuciya ɗaya, mayar da hankali kan abubuwan da ke da muhimmanci maimakon son zuciya da rashin fahimta.”

“Majalisar tarayya sau biyu tana amincewa da ƙudirin neman korar hafsoshin tsaro. Shugaban ƙasa Buhari ya gaya wa majalisar tarayya ta tara da ta mayar da hankali kan aikin da ke gabanta. Idan an fassara abun da kyau, kiran da majalisar ta yi na ɓata dimokuraɗiyya da sojoji ne.”

“Wannan ya kamata ya zama darasi ga ƴan siyasa. Rigima ce kai tsaye zargin hafsoshin tsaro kamar su ne suka fara rashin tsaro. Matsalar rashin tsaro da ake fuskanta a ƙasar nan tun shekarar 2009 ƴan siyasa ne suka kirkiro ta. Indai da gaske a ke, za a iya kawo ƙarshen matsalar.”

Ya shawarci ƴan siyasa da ma’aikatan gwamnati da su cigaba da rayuwa ta hanyar gujewa cin hanci da rashawa wanda a cewarsa, ya dabaibaye harkar siyasar kasar nan tsawon shekaru da dama, tare da zubar da mutuncin jama’a da hana samun cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button