Labaran Hausa

Da Dumi Dumi: Yan bindiga sun bukaci miliyan 53 kudin fansar Fasto da wasu mutum 2 Da…

Da Dumi Dumi: Mahara Sun Bukaci Miliyan 53 Kudin Fansar Malamin Addini da Wasu Mutum 2 a Jihar Arewa

Kwanaki kadan bayan sace shahararren Fasto da wasu mutane biyu a Kwara, maharan sun bukaci kudin fansa miliyan 53.

Dagacin kauyen Agbeku, Oba Abdulazeez Shola shi ya tabbatar da haka ga manema labarai inda ya ce an fara bincike kan lamarin.

Idan ba a mantaba, a ranar Asabar ce 11 ga watan Nuwamba ‘yan bindigan suka sace Faston da wasu mutane biyu a jihar Kwara.

Masu garkuwa da su ka sace Fasto da wasu mutane biyu sun bukaci kudin har naira miliyan 53.

Maharan sun sace mutanen uku ne a karamar hukumar Ifelodun da ke jihar Kwara a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, cewar Trust Radio.

Daga cikin wadanda aka sacen akwai Rabaran S. B Oladunni wanda shi ne shugaban cocin Igabala DCC da kuma wasu mutum biyu.

Mai sarautar gargajiya na Agbekuland, Oba Abdulazeez Shola ya tabbatar da sanarwar kudin fansar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba ga manema labarai.

Ya ce rundunar ‘yan sanda a jihar ta fara bincike kan lamarin don samun bayanai da kuma dakile faruwar hakan a gaba.

Ya ce: “Yayin da aka gindaya miliyan 20 kan Faston, miliyan 30 ne daya matar za ta biya yayin da mutum na ukun zai biya miliyan 3.”

Daily Trust ta tabbatar cewa jami’an ‘yan sanda sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da hannu a cikin satar mutanen a jihar Kwara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Back to top button